Matatar Dangote ta kara sama da Naira 100 a kan kowacce lita

Pump 2

Matatar mai ta Dangote ta kara farashin lita, da N101, inda ta daga farashin baya na Naira 774 zuwa Naira 875 kan kowace lita a matakin ex-depot, lamarin da ya tayar da fargaba kan yiwuwar karin farashin man fetur a fadin kasar.

Wani babban jami’in matatar ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, yana mai danganta hakan da tashin gwauron zabi da ake samu a farashin danyen mai a kasuwannin duniya a baya-bayan nan.

Karin farashin ya zo ne jim kadan bayan matatar ta dakatar da lodin fetur daga karfe 12:00 na dare na ranar 2 ga Maris, 2026, sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya wanda ya haura dala 80 kan kowanne ganga a cikin dare.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin masana’antu sun nuna cewa an dakatar da lodin mai daidai karfe 12:00 na dare, tare da tsayar da daukar kaya da kuma fitar da takardun, alamar cewa an dakatar da sabbin hada-hadar ciniki na dan lokaci.

Sai dai dakatarwar ta shafi fetur ne kawai, yayin da aka ci gaba da lodin dizal.

Matakin da matatar ta dauka ya jawo martani daga bangaren dillalan man fetur, inda wasu masu rumbunan ajiya masu zaman kansu a fadin kasar suka dakatar da sayar da mai a ranar ciniki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here