Iyalan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun karyata zarge-zargen da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta yi na cewa an gano na’urorin satar sauraron waya masu inganci a gidansa.
A wata sanarwa da Mohammed Bello El-Rufai, ɗan Malam El-Rufai kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, ya sanya wa hannu ranar Litinin, iyalan sun bayyana zargin a matsayin “ƙarya karara” tare da zargin hukumar da gudanar da yaƙin neman suna a kafafen yada labarai maimakon bin ka’idojin doka.
SolaceBase ta ruwaito cewa ICPC ta ce ta gano wasu kayayyaki da ake zargin suna iya satar sauraron tattaunawa da takardun tsaro masu muhimmanci daga gidan tsohon gwamnan da ke Abuja.
Hukumar ta ce an kwato dukkan kayayyakin da ake zargi a gaban matar tsohon gwamnan, Hadiza, da kuma ɗansa, Mohammed.
Mohammed Bello El-Rufai, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Dokokin Bankuna, ya ce iyalan sun kauce wa yin magana a bainar jama’a ne domin mayar da hankali kan watan Ramadan, amma sun ga ya zama dole su mayar da martani.
Sanarwar ta ce, ICPC ta yi ƙoƙarin amfani da shiru na mahaifinmu a matsayin makami a kansa, tana zargin cewa ya ƙi bayar da hadin kai.
Iyalan sun jaddada cewa a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, kowane ɗan ƙasa yana da ’yancin yin shiru, tare da cewa amfani da wannan hakki ba alamar rashin bayar da hadin kai ba ne.
Rahotanni sun ce, Malam Nasir El-Rufai na cewa, a gurfanar da shi a kotu idan ana da wani abu a kan sa.
Sanarwar ta kuma tabo batun zargin na’urorin satar sauraron waya da aka ce an kwace yayin samamen da ICPC ta kai gidansa.
Iyalan sun ce kayayyakin da aka kwace sun takaita ne ga tsofaffin wayoyin hannu na kashin kai, faifan ajiya (flash drives), da kwamfutoci masu ɗaukuwa (laptops) — ba wai wasu manyan na’urorin leƙen asiri ba kamar yadda hukumar ta bayyana.
Sanarwar ta kuma yi zargin cewa samamen da ya kai ga kwace kayayyakin ya dogara ne kan sammaci mara inganci.
Iyalan sun tabbatar da cewa lauyoyinsu sun kalubalanci wannan sammaci a kotu mai hurumi.













































