Gwamna Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC

Screenshot 2026 02 27 092241 645x430

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, yana mai cewa muradun al’ummar jihar ne suka sa ya ɗauki matakin.

Da yake jawabi a wani saƙon kai tsaye ga al’ummar jihar a safiyar Juma’a, Fintiri ya jaddada cewa matakin ya samo asali ne daga burin tabbatar da jin daɗi da ci gaban al’ummar Adamawa.

“Wannan sauya sheƙa ta ta’allaka ne kan tabbatar da jin daɗi da ci gaban al’ummarmu. Ina roƙon kowa da ya tsaya tsayin daka tare da bai wa gwamnati goyon baya da fahimta domin a cimma ribar dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, tare da yin alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya domin samar da sakamako mai amfani ga jihar.

Sanarwar Fintiri ta kawo ƙarshen makonnin jita-jita kan inda siyasar sa ta dosa, inda ta tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here