EFCC ta sake gurfanar da Malami, matarsa da ɗansa kan zargin badaƙalar kuɗi

images 12 (1)

Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a ranar Juma’a ta sake gurfanar da tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, SAN, tare da matarsa, Asabe Bashir da ɗansa, Abdulaziz, bisa zargin aikata laifukan wankiyar kuɗi.

An sake gurfanar da su ne a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja, bayan an sauya wa shari’ar alkali.

Da aka ci gaba da sauraron shari’ar, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, SAN, ya shaida wa kotu cewa an kawo ƙarar a karon farko a gabanta, inda ya roƙi a karɓi amsar tuhumar daga waɗanda ake ƙara.

Haka kuma ya nemi a gyara adadin kuɗin da ke cikin tuhume-tuhume na 11 da 12, inda ya ce a maimakon Naira Biliyan 325 a rubuta Naira Miliyan 325 a tuhume na 11, sannan a maimakon Naira Biliyan 120 a rubuta Naira Miliyan 120 a tuhume na 12.

Lauyan masu kare kai, Joseph Daudu, SAN, bai yi adawa da buƙatar ba, kuma kotu ta amince da gyaran.

Sai dai Malami, matarsa da ɗansa sun musanta tuhume-tuhume guda 16 da EFCC ta gabatar a kansu, waɗanda suka shafi zargin wankiyar kuɗi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa wata alkaliya, Mai shari’a Obiora Egwuatu, ta janye daga shari’ar a ranar 12 ga Fabrairu, jim kaɗan bayan an miƙa mata ƙarar.

Tun da farko shari’ar na gaban Mai shari’a Emeka Nwite ne, wanda ya zauna a matsayin alkalin hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Bayan hutun, Babban Alƙalin Kotun Tarayya ya sake rabon shari’o’in zuwa hannun Mai shari’a Egwuatu, wadda daga baya ta janye, kafin a sake miƙa su ga Mai shari’a Abdulmalik.

An fara gurfanar da Malami, matarsa da ɗansa a ranar 30 ga Disamba, 2025.

Yayin da aka tsare Malami da ɗansa a Gidan Yari na Kuje, an tsare Asabe a Gidan Yari na Suleja, kafin daga bisani a ba su beli na Naira Miliyan 500 kowannensu tare da sharadin mutum biyu da za su tsaya musu a irin wannan adadi. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here