Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa ‘ya’yansa biyu, Mustapha da Ummi, a wani mummunan hadarin mota.
‘Yan uwan sun rasu ne a ranar Asabar lokacin da abin hawan da suke ciki ya yi hadari a kan hanyar Bauchi zuwa Azare yayin da suke dawowa Bauchi daga Azare, hedikwatar Karamar Hukumar Katagum.
An ruwaito cewa an tabbatar da rasuwarsu ne bayan sun samu munanan raunuka a hadarin.
A halin yanzu, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya jajantawa Sanata Tela da iyalinsa bisa wannan rashi.
A cikin sakon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin na bakin ciki, yana mai cewa rasuwar ‘ya’yan biyu babban rashi ne ga iyali da kuma jihar.
Ya ce wannan mummunan lamari ya jefa iyalin Tela cikin bakin ciki kuma ya bayyana jin tausayi a gare su a wannan lokaci mai wahala.
Gwamna Mohammed ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan kurakurensu, Ya ba su Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalin da aka yi wa rashi karfi da juriyar jure wannan babban rashi.
An yi sallar jana’izar Mustapha da Ummi a Fadar Sarkin Bauchi a ranar Lahadi da karfe 11:00 na safe.













































