Gwamna Yusuf ya yi wa Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarsa

images 62

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon ta’aziyya ga Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, bisa rasuwar mahaifiyarsa Alhaja Sidikat Basiru, wadda ta rasu tana da shekaru 92 a duniya.

Hakan na kunshe a cikin sakon ta’aziyyar da daraktan yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin a Kano.

A cikin sakon, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayiya Alhaja Sidikat Basiru a matsayin musulma mai biyayya, mahaifiya mai tausayi kuma abar misali wadda rayuwarta ta kasance cikin tawali’u, mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki da sadaukar da kai ba tare da son rai ba.

Gwamnan ya ce kyawawan dabi’u da jajircewar da ta yi wajen tarbiyyar ‘ya’yanta da kyawawan dabi’u da na addini, a bayyane yake a cikin halayya da hidima ta musamman da Sanata Basiru da sauran ‘ya’yanta ke yi.

Ya ce marigayiya Alhaja Sidikat Basiru ta rayu rayuwa mai tasiri, ta kuma bar gado na imani, gaskiya da hidima da zasu ci gaba da zama abin koyi ga tsararraki masu zuwa.

Gwamna Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, dukan iyalin Basiru, abokai da makusanta, inda ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki SWT ya ba su hakuri da juriyar daukar wannan babban rashi da ba za a iya cike wa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here