Gwamnatin Kaduna za ta dauki nauyin iyalin matar da mutane suka yi wa kisan gilla – Gwamna Sani

images 61

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da iyalin marigayiya Ummulkhairi Aliyu, matar da wasu mutane suka yi wa kisan gilla a Maraban Jos, karamar hukumar Igabi ta jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta dauki nauyin kula da mijin marigayiyar da ‘ya’yanta hudu, ciki har daukar nauyin karatun yaran.

Sani ya yi wannan alkawarin ne a ranar Asabar lokacin da ya kai ziyar ta’aziyya ga iyalin da aka yi wa rashi a Maraban Jos, kusan makonni biyu bayan an kashe ta.

Marigayiya Ummulkhairi malamar addinin Islama ce da wasu fusatattun mutane suka yi wa duka ha rya yi sanadiyyar mutuwarta a ranar 14 ga watan Yuni bisa zargin cewa ta yi yunkurin sace yara.

Bayan haka aka kone gawarta kafin jami’an tsaro su dawo da zaman lafiya a yankin.

Da yake jawabi yayin ziyar, gwamnan ya yi Allah-wadai da ayyukan daukar doka a hannu, yana mai bayyana su a matsayin al’adar dabbobi, tare da tabbatar wa iyalin cewa za a yi adalci.

Ya ce, “Bana Jihar Kaduna a lokacin da wannan mummunan lamarin ya faru saboda ina kan wani aiki, amma nan take na ba da umarni ga manyan jami’an gwamnati su ziyarci iyalin su yi musu ta’aziyya.

“Har ila yau, ina so in tabbatar muku cewa Gwamnatin Jihar Kaduna za ta dauki nauyin iyalin. Za mu tallafa wa mijin ta kuma mu tabbatar cewa ‘ya’yanta hudu sun samu ingantaccen ilimi.”

Gwamnan ya bayyana cewa yana aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a kisan.

A cewar sa, “Ina aiki tare da Kwamishinan ‘Yan Sanda, Darakta na Hukumar Tsaro ta DSS da dukkan hukumomin tsaron da suka dace a Jihar Kaduna don gano musabbabin lamarin.

“Na yi farin ciki da cewa sun gudanar da bincike sosai kan wannan lamari. Kamar yadda muke magana yanzu, an kama mutane kusan 41 da laifin kisan kai.

Ya yi alkawarin cewa ba za a bar duk wanda ke da hannu a kisan duk matsayin.

Yayin da ya yaba wa hukumomin tsaro kan yadda suka yi sauri da binciken da suke ci gaba da yi, Uba Sani ya ba da umarnin a yi bincike sosai kan wasu jami’an tsaro, musamman Baturen ‘Yansanda (DPO) da ke kula da Maraban Jos.

Ya ce duk wani jami’in da aka samu ya yi sakaci ko ya sabawa binciken, za a kama shi da alhaki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here