DA DUMI-DUMI: Darakta Janar na kungiyar gwamnonin APC ya yi murabus saboda takaddama kan babban taron jam’iyyar

Salihu Lukman
Salihu Lukman

Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC, Salihu Lukman, ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus din nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan babban taron jam’iyyar APC da ke shirin yi.

Ko da yake Lukman bai mayar da martani ga manema labarai ba kan dalilin da ya sanya yayi murabus. Amma wani jami’in jam’iyyar ya ce “shugaban PGF ya yi abin da ya dace ta hanyar yin amfani da hankali domin magancewa kasansa matsalar da zai iya fuskanta”.

An rahotanni sun bayyana cewa murabus din nasa ya biyo bayan taron kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC a daren Lahadi inda wasu daga cikin gwamnonin suka bukaci a tsige shi saboda yawan surutu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here