Cika shekara 74: Tinubu ya bayar da dukkan albashinsa ga asusu na musamman na rundunar soji

Tinubu new 1 (1)

Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Lahadi a Abuja, ya kaddamar da wani asusu na musamman domin tallafa wa sojojin da suka jikkata da kuma iyalan wadanda suka rasu, a matsayin wani bangare na bikin cikar sa shekara 74 da haihuwa.

Tinubu ya bayyana cewa asusun zai kula da sojojin da suka samu raunuka yayin aiki, tare da iyalan jami’an tsaro da suka rasa rayukansu yayin kare kasa.

Ya ce, ya umarci Akanta-Janar na Tarayya da ya bude wani asusu na musamman domin kula da kudaden, domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen rabon kudaden.

Shugaban ya kuma sanar da cewa zai bayar da dukkan albashinsa tun bayan hawansa mulki a matsayin kudin farko na fara wannan asusu.

Ya ce wannan shiri zai kara karfafa tsare-tsaren inshora da jin dadin rayuwar sojoji da ake da su a halin yanzu.

Ya kara da cewa asusun zai tallafa kai tsaye ga sojojin da suka rasa gabobinsu da kuma iyalan wadanda suka sadaukar da rayukansu domin tsaron kasa.

Tinubu ya bayyana cewa wadanda za su amfana sun hada da zawarawa, mazajen da suka rasa matansu, da kuma ‘ya’yan jaruman da suka mutu wajen kare kasa.

Ya yi kira ga gwamnoni, ‘yan majalisar dokoki, kamfanoni masu zaman kansu da sauran ‘yan kasa masu hali da su goyi bayan wannan shiri.

Ya ce nan gaba kadan za a bayyana cikakken bayani kan asusun domin bai wa mutane da kungiyoyi damar bada gudummawa.

Shugaban ya jaddada muhimmancin girmama da tallafa wa jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
Ya bayyana wannan shiri a matsayin wani nauyi na kasa, ba wai sadaka ba, yana mai cewa dole ne a cika wannan alhaki.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here