SSANU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kammala yarjejeniyar da suka ƙulla a 2009

SSANU SABO

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, ta ba gwamnatin tarayya wa’adin watan Afrilu domin kammala sake tattaunawar yarjejeniyar shekarar da suka ƙulla a 2009.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa bayan kammala taron kwamitin zartarwarta na kasa karo na 54 da aka gudanar a Jami’ar Jihar Ekiti da ke Abuja.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban SSANU na kasa, Muhammad Ibrahim.

Ibrahim ya yi gargadin cewa rashin kammala yarjejeniyar sake tattaunawa ta 2009 na iya haifar da yajin aiki mara iyaka.

Ya nuna damuwa kan jinkiri da rashin kammala tattaunawar da ake yi da kungiyoyin ma’aikatan da ba na koyarwa ba, yana mai cewa babu takamaiman jadawalin lokaci ko tabbacin kudurin gwamnati.

Ya ce dole ne gwamnati ta sake zama domin kammala wannan tattaunawa cikin adalci, gaskiya da kuma kayyade lokaci ba tare da bata lokaci ba.

Ya kara da cewa daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 30 ga Afrilu, 2026, kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adi na karshe domin kammala yarjejeniyar tare da sanya hannu.

Ya bayyana cewa idan gwamnati ta kasa yin hakan cikin wannan lokaci, kungiyar za ta hada kai da abokiyar aikinta a kwamitin hadin gwiwa na JAC wanda ya kunshi NASU da SSANU domin fara yajin aiki mara iyaka.

Haka kuma, ya soki jinkirin biyan albashi da rashin biyan karin albashi, yana mai cewa hakan ya kara jefa mambobinsu cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci a gaggauta biyan dukkan basussukan albashi tare da amfani da tsari guda na biyan albashi, inda ya ba da shawarar amfani da tsarin Remita.

Shugaban ya kuma yi zargin cewa wasu rukunin ma’aikata an cire su daga cikin kudin alawus na Naira Biliyan 50 da aka amince da shi a shekarar 2022, yana mai jaddada cewa dole ne a hada dukkan ma’aikatan da suka cancanta ba tare da wariya ba.

Ibrahim ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar sake duba albashi da kuma karfafa tsare-tsaren tallafin jin kai.

Ya kuma nuna damuwa kan karancin kudaden da ake bai wa jami’o’i, yana mai danganta hakan da lalacewar ababen more rayuwa da kuma tabarbarewar ayyukan da ake bayarwa.

Haka zalika, ya bayyana damuwa kan matsalar tsaro a harabar jami’o’i da ma fadin kasar, yana mai kira da a inganta sa ido da kuma tsaron ma’aikata da dalibai.

Ya yi gargadin cewa raunin tsarin fasahar zamani da karancin kudaden bincike na iya rage karfin gasa na ilimin Najeriya a duniya.

Ya kuma yi watsi da tsarin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da zai iya jawo asarar ayyukan yi, tare da kira da a ci gaba da tattaunawa ta hanyar kafa tsayayyen tsarin tuntuba domin kauce wa rikice-rikicen masana’antu.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here