An yi jana’izar mahaifiyar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a Abuja, inda manyan ‘yan siyasa na Najeriya, attajirai da sarakunan gargajiya suka halarta.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mahaifiyar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, Hajiya Umma, ta rasu ne a ranar Juma’a a kasar Masar bayan fama da jinya mai tsawo.
Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja akwai Atiku Abubakar, Nuhu Ribadu, Uba Sani, Aliko Dangote, Sarkin Kano na 1
6 Muhammadu Sunusi na II, da Sarkin Zazzau Nuhu Bamalli, tare da sauran manyan mutane.
Sallar jana’izar ta kuma samu halartar dimbin shugabannin siyasa daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da gwamnoni, sanatoci da ‘yan majalisar dokoki ta kasa.

Halartar ‘yan siyasa daga bangarori daban-daban ya nuna hadin kai da alhini tare, yayin da masu ta’aziyya suka taru domin yi wa mamaciyar bankwana da kuma nuna goyon baya ga iyalan El-Rufai.
An gudanar da addu’o’i domin Allah ya jikanta da rahama, yayin da mahalarta suka jajanta wa iyalanta tare da karfafa musu gwiwa su ci gaba da jure wannan lokaci na jimami.













































