Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar bayan aƙalla shekara huɗu a cikinta.
Matakin na zuwa ne bayan da manyan jiga-jigan adawar Najeriya ke ƙoƙarin ƙulla wani ƙawancen siyasa domin ‘kawar da jam’iyyar APC a 2027’
Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga NNPP ne la’akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki, wanda ke bukatar haɗin kai.
”Matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wasu jam’iyyun don kawo wa ƙasarmu sauyi nagari”, kamar yadda Kwankwason ya bayyana.












































