Atiku, Malami, Amaechi sun kaiwa Elrufa’i ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Malami Atiku 1

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana nan daram cikin imani kuma bai karaya ba duk da rasuwar mahaifiyarsa kwanan nan.

Atiku ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar bayan jagorantar wata tawaga domin kai ziyara ta ta’aziyya ga El-Rufai a gidansa da ke Abuja.

Ya ce ziyarar ta kasance ne domin nuna goyon baya ga tsohon gwamnan da iyalansa bisa wannan rashi mai raɗaɗi da babu wanda zai maye gurbinsa, na mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai.

Ya bayyana cewa yana tare da shi cikin wannan raɗaɗi tare da yin addu’ar Allah ya jikanta da rahama.

Atiku ya kara da cewa ya samu karfin gwiwa ganin yadda El-Rufai yake da natsuwa da juriya duk da wannan hali na alhini.

Ya ce ya karfafa masa gwiwa da ya ci gaba da tsayawa da kafafunsa, domin wannan ma zai wuce.

Haka kuma, tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami SAN, ya kai wata ziyara ta daban domin jajanta masa, inda ya nuna alhininsa kan wannan rashi.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Malami ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama tare da bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.

Ya kara da cewa yana tare da El-Rufai da iyalansa a wannan lokaci na jimami.

Sauran manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, sun kuma kai ziyara ko tura sakonnin ta’aziyya ga tsohon gwamnan.

Ziyaran na zuwa ne yayin da iyalai, abokai da masu alaka ke ci gaba da jimamin rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, tare da yin addu’ar Allah ya sa ta huta lafiya.

A wani bangare, Malam El-Rufai ya isa gidansa da ke Abuja bayan Hukumar ICPC ta sake shi na dan lokaci bisa dalilan jin kai domin halartar jana’izar mahaifiyarsa.

Ta rasu ne a birnin Cairo na kasar Masar a ranar Juma’a bayan fama da jinya.

El-Rufai yana tsare a hannun ICPC tun daga ranar 18 ga watan Fabrairu bisa zargin wasu laifuka da suka shafi harkokin kudi da sauran batutuwa masu alaka.

Haka kuma yana fuskantar wata shari’a ta daban daga hukumar DSS kan zargin yin amfani da na’urar sauraren wayar wani jami’i, wanda ya shafi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 23 ga watan Afrilu domin gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan shari’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here