Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya ce tun da aka rantsar da shi har zuwa wannan lokaci a cikin bashi yake mulki, saboda gadar mulki ba tare da kudi ba a asusun gwamnati.
Gwamnan Lawan a wata tattaunawa ta musamman da BBC, ya yi bayani a kan yadda ya tarar da gwamnati bayan ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu har zuwa wannan lokaci.
Ya ce babu wani abin da gwamnatinsa ta tarar a cikin lalitar Zamfara, sai naira miliyan uku kacal.
“Kusan asusu guda na gani, watakila ince akwai kamar naira miliyan uku ko hudu ne a ciki”, in ji Dauda.
Ya ce a halin yanzu yana bige-bigen neman rance domin samun kuɗin biyan ma’aikata albashi watanni hudu da suke bin gwamnati.
Gwamnan Dauda da ke fayyace dalilan da suka sanya suke binciken tsohon gwamnan da nazartar yadda abubuwa suke a Zamfara ya ce a halin yanzu babu wuta a ma’aikatun gwamnati saboda ana binsu bashi na miliyoyin naira.
Sannan suma jami’an tsaro an daina biyansu kuɗaɗen alawus-alawus wata da watanni, harkar ilimi ya durkushe baki-daya.
“Yau da mu ke maganar nan duk wani dalibi na jihar Zamfara, bai rubuta jarabawar NECO da WAEC ba, saboda ana bin gwamnati kuɗi fiye da naira biliyan ɗaya”.













































