Ba ma neman Matawalle ruwa a jallo – EFCC

1687099863440
1687099863440

Hukumar da ke yaƙi da yi wa arziƙin ƙasa ta’annati EFCC ta ce ba ta neman tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ruwa a jallo.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter EFCC ta ce ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jan hankalinta da aka yi kan rahoton wata jarida da ta wallafa a ranar Lahadi 18 ga watan Yunin nan da muke ciki da ke cewa tana neman Matawalle ruwa a jallo.

“Hukumar EFCC ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ruwa a jallo ta kuma nemi hukumar tsaro ta fararen kaya DSS ta kama shi “duk inda aka ganshi”, kamar yadda yake cikin sanarwar.

EFCC ta ce rahoton ba daidai ba ne, ya zuwa yanzu ba ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ba, ko neman DSS ta kama mata shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar na da tsarukanta da take bi ta ayyana mutum a matsayin wanda take nema, kuma tana da hanyoyin da take bi ta sanar da mutane tana neman shi, ba ta hanyar amfani da majiyoyin bogi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here