Kungiyar Manoma ta Kasa AFAN, reshen Jihar Kano ta bayyana rashin jin dadinta kan tsadar taki, inda ta jaddada bukatar gaggawa na gwamnati ta ba da tallafin kayan aikin noma don bunkasa aikin gona.
Shugaban kungiyar, Abdullahi Ali-Maibread ne ya yi wannan kira a wata hira da manema labarai a ranar Talata a Kano kan shirye-shiryen aikin noma na 2026.
Ya nuna damuwarsa cewa manoman Kano ba su samu tallafi daga kowane matakin gwamnati ba har yanzu.
Saboda haka Shugaban ya jaddada bukatar gwamnati ta bada tallafi cikin gaggawa wajen rarraba ingantattun iri da taki a farashi mai rahusa, da kuma tabbatar da matakan tsaro don kare manoman da ke aiki a gonakinsu.
Ya ce kungiyar na aiki tare da wasu masu ruwa da tsaki don tabbatar manoma sun samu ingantattun iri da magungunan kashe ciyayi da kwari cikin lokaci domin samun girbi mai yawa.
“Muna kuma karfafa manoma kan ayyukan noma na jure sauyin yanayi da magudanar ruwa yadda ya kamata, don rage hadarin ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a lokacin ruwan sama mai yawa,” in ji shi.
Ali-Maibread ya kara da cewa kungiyar na kara wayar da kan manoma kan yadda za a magance kwari, sannan suna tattaunawa da jami’an tsaro domin kare gonaki a lokacin noma.
A halin da ake ciki, wasu manoman da aka tattauna da a karamar hukumomin Gezawa, Warawa da Gabasawa suma sun nuna damuwa kan hauhawar farashin taki da sauran kayan aikin gona, inda suka ce hakan ka iya haifar da raguwar samun girbi.
Malam Muntari Al-hassan, manomin masara da gero, ya koka kan yadda farashin buhun NPK ya tashi daga kusan N35,000 a bara zuwa sama da N51,000 a wannan shekarar.
Ya bayyana cewa saboda tsadar takin, zai rage yawan noman da yake daga hekta 12 zuwa 7 domin kauce wa asara mai yawa.
A nata bangaren, Hajiya Nusaiba Bako, manomiyar kayan lambu, ta ce mata manoma da yawa na iya barin noma a bana saboda ba za su iya sayan kayan aiki ba a yanzu, musamman taki.
Wani manomi a Gabasawa, Aliyu Lawal, ya shaida wa kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) cewa ba zai iya noman masara a wannan shekarar ta 2026 ba saboda tsadar taki.
“Ba zan iya shuka masara a wannan shekarar ba saboda tsadar taki, zan fi shuka gero, kuma ma sai na dogara da takin gargajiya don daidaita,” in ji shi.
Manoman sun kuma roki Gwamnatin Kano da Ma’aikatar Noma ta Tarayya da su dauki mataki kan masu siyar da takin bogi, da tabbatar da rarraba takin tallafi kai tsaye ga manoma.











































