Majalisa ta 10: ‘Yan adawa sun kafa kwamitin mutane 11 dan fidda dan takarar su.

A halin da ake ciki gamayyar ‘yan adawa zababbun ‘yan majalisar wakilai sun kafa wani kwamiti da zai tantance tare da zabo ‘yan takarar da za su tsaya takarar shugabannin majalisa ta 10.

A cikin wata sanarwa da zababbun mambobin suka fitar sun bayyana Dan majalisa Nicholas Mutu a matsayin shugaban kwamotin da kuma dan majalisa Victor Ogene a matsayin sakataren kwamitin mutum 11.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Ogene da wasu mambobin kungiyar uku, ta ce kwamitin na da mako guda ya gabatar da rahotonsa.

Mambobin da suka fito daga jam’iyyu takwas sun ce suna da mambobi 183, suna da abin da ake bukata wajen samar da shugaban majalisar sabanin ‘yan jam’iyyar APC 173.

“A bisa yarjejeniyar bai daya da jam’iyyun siyasarmu suka kulla da al’ummar Najeriya, wato rike gwamnati da jama’a, mun kuduri aniyar shiga cikin fage, ta hanyar bayar da sahihin zabin shugabanci.

“A bisa wannan kuduri, “Mafi rinjaye” na majalisar wakilai ta 10, sun hada da wani kwamiti mai mutum 11 – wanda shugaba da sakatare wanda aka dorawa alhakin tantancewa da kuma ba da shawarwarin masu neman kujerar shugaban majalisar da mukaman mataimakin kakakin majalisa.

Mambobin kwamitin sun hada da Dan majalisa Abdulmumini Jibrin, mataimakin shugaban kwamitin (NNPP) Rep. Oluwole Oke (PDP) dan majalisa Gaza Jonathan Gbefwi (SDP) da kuma dan majalisa Beni Lar (PDP).

Sauran sun hada da, Dr Ali Isa (PDP) Rep. Kabiru Rurum (NNPP) Rep. Donatus Mathew Kuzalio (LP) Rep. Yusuf Salisu Majigiri (PDP) Rep. Nnabuife Chinwe Clara (YPP) Rep. Maureen Chinwe APGA, Rep. Idris Salman (ADC) da kuma Rep. Afam Ogene Secretary (LP)

Kamfanin dillacin labaran Najeriya ya rawiato cewa APC ce ke da rinjaye a Majalisar Wakilai da kujeru 175 yayin da PDP ke da 118 sai LP ke da 35.

Jam’iyyar NNPP tana da kujeru 19. APGA na da kujeru biyar, yayin da SDP da ADC ke da kujeru biyu kowanne yayin da YPP ke da kujera daya

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here