A yau Alhamis ne jam’iyyar APC ta kafa kwamitocin da zasu jagoranci gudanar zaben shiyoyin kasar nan, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 12 ga Maris.
Sanata John Akpanudoedehe, sakataren jam’iyyar APC na riko ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
“Shugabannin kwamitocin dukkansu mambobin kwamitin riko na jam’iyyar ne, yayin da aka zabo sakatarorin daga cikin mataimakan gwamnoni daga ko wace shiyya .
“Taro na masu ruwa da tsaki na ko wace shiyya zai gudana ne a ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu,” in ji Akpanudoedehe.
A cikin jerin sunayen da sakataren kasa ya fitar, Alhaji Abubakar Bello ne zai jagoranci kwamitin arewa ta tsakiya, Sanata Yusuf Yusuf Arewa maso Gabas da Sanata Abba Ali Arewa maso Yamma.
Har ila yau, Sanata Ken Nnamani ne zai jagoranci kwamitin Kudu maso Gabas Mista David Lyon Kudu maso Kudu da kuma Aknremi Olaide Kudu maso Yamma.
A yayin babban taron na shiyoyi za’a zabi shugabannin jam’iyyar na shiyyar gabanin babban taron kasa da aka shirya yi a ranar 26 ga watan Maris.
Ana sa ran za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa a babban taron da za su tafiyar da harkokin jam’iyyar wanda a halin yanzu Gwamna Mai Mala Buni ke jagoranta a matsayi na riko.













































