A gaggauta kwashe ‘yan Najeriya dake Ukraine – Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya

FCDE85EF 9693 46B3 BC36 FE08B83A891A
FCDE85EF 9693 46B3 BC36 FE08B83A891A

A yau Alhamis ne majalisar wakilai ta bukaci a kwashe ‘yan Najeriya da ke Ukraine cikin gaggawa.

Idan za a iya tunawa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar alhamis ya sanar da kai wani farmakin soji a kasar Ukraine tare da jin karar fashewar wasu bama-bamai a duk fadin kasar, inda ministan harkokin wajen kasar ya yi gargadin cewa ana ci gaba da kai wani gagarumin farmaki.

Sai dai ‘yan majalisar sun nuna damuwarsu kan cewa akwai dalibai ‘yan Najeriya da dama a Ukraine da za su iya shiga cikin tashin hankali.

Dan majalisa Ahmed Munir ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar a ranar Alhamis.

Sai dai wasu ‘yan majalisar na fargabar cewa watakila ya makara domin ya kamata a ce an dade ana kwashe mutanen.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya amince da wani dan majalisa, Leke Abejide, ya tattauna da shugaban kamfanin jirgi na Air Peace, Allen Onyema don kwashe ‘yan Najeriya daga Ukraine daga yau zuwa ranar Litinin, 28 ga watan Fabrairu.

An umarcu Kwamitin Majalisar mai kula da kan harkokin kasashen waje da yayi aiki da ma’aikatar kasashen wajen domin samun nasarar wannan aikin dawo da ‘yan Najeriya dake Ukraine.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here