Kasa da kwanaki 12 kafin zaben Najeriya, Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, tace ba za a yi zabe a rumfunan zabe 240 ba.
Shugaban Hukumar zaben ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a ranar Litinin.
Yakubu ya ce babu wanda ya zabi kada kuri’arsa a wadannan rumfunan zaben.
Karin bayani na tafe….












































