Tinubu ya tsawaita wa’adin CGC Adeniyi tsawon watanni shida

Bola Tinubu signs 750x430

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin wa’adi na karshe na tsawon watanni shida ga Shugaban Hukumar Hana Fasakwauri Adewale Adeniyi.

Wa’adin farko na Adeniyi a matsayin Shugaban hukumar zai kare ranar 1 ga Agusta, 2026.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, wadda mai baiwa Shugaban Kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, karin watanni shida din, wanda zai kare a watan Fabrairu 2027, domin ba shi damar kammala aiwatar da tsarin “National Single Window” da tabbatar da sauya mika mukami cikin tsari a hukumar.

“A yayin mika mukamin, Adeniyi, tare da Hukumar Gudanar ta Hukumar ta NCS, za su tabbatar da daga murtabar cantattun jami’ai zuwa matsayin Kwamturola da kuma tilasta ritaya ga jami’an da suka kai shekaru 60 ko suka yi shekaru 35 aiki.”

“Adeniyi ya shiga aikin Kwastam bayan kammala karatu daga Jami’ar Obafemi Awolowo a karshen shekarun 1980.

“Ya hau matakai har ya zama Mataimakin Kwamturola a 2012, Kwamturola a 2017, kafin Shugaba Tinubu ya nada shi a matsayin Shugaban Hukumar a watan Yunin 2023,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here