Rahotanni na bayyana cewa ‘yan Najeriya dari hudu da aka kora daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun iso gida Najeriya, kamar yadda gidan talabijin na Najeriya (NTA) ya bayyana.
Jami’an ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira, hukumar hana fataucin mutane ta kasa ne suka tarbi mutanen a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Rahotanni sun bayyanna cewa an dawo da kimanin ‘yan Najeriya dari hudu da suka hada da mata 90 da maza 310 daga Hadaddiyar Daular Larabawan zuwa Najeriya.
“An tarbe su ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira, hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP), Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da sauran masu ruwa da tsaki,” in ji wata sanarwa da ta fita a ranar Laraba.
A watan Yuni, bayan tattaunawa da dama da hukumomin UAE, gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ‘yan kasar cewa nan ba da jimawa ba za a dage haramcin biza.
A daidai wannan lokaci ne aka bayyana cewa Najeriya ta biya kashi 98 cikin 100 na dala miliyan 850 da ake bin kasar, lamarin da ke nuna an samu ci gaba wajen warware takaddamar.