Gwamnatin Kano ta sanya sabbin ranakun bude makarantun firare da sakandire

Abba Kabir Yusuf 1 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta amince da sabbin ranakun sake bude makarantu na gwamnati da masu zaman kansu na firamare da sakandire gaba na shekarar 2024/2025.

Dangane da sabunta jadawalin, daliban kwana za su koma makaranta ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, yayin da daliban da daliban da ke zuwa makarantun rana za su koma ranar Litinin, 16 ga Satumba, 2024.

Wannan sanarwar ta biyo bayan dage dawo da makarantu tun da farko, wanda kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayar a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba.

A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ranar Alhamis, an bukaci iyaye da masu kula da su da su tabbatar da bin sabbin ranakun.

Sanarwar ta kuma shawarci dalibai da su guji kawo abubuwan da aka haramta, kamar wukake ko reza, da kuma bin ka’idojin makaranta.

Gwamnati karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta jaddada kudirinta na samar da ingantaccen ilimi da samar da yanayi mai kyau na samun nasarar karatu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here