Gwamna Umaru Bago na Neja ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fara biyan ma’aikata mafi karancin albashi na Naira 70,000 matukar akwai wadatar fara biyan.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai bayan bude taron wakilan kungiyar likitoci da ma’aikatan lafiya na Najeriya (MHWUN) na shekara hudu na shekara ta 2024 a Minna ranar Laraba.
Bago, wanda mataimakinsa, Mista Yakubu Garba ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar na jiran aiwatar da shi tsarinne a matakin kasa.
“Batun mafi karancin albashi shi ne yarjejeniyar da aka yi, muna jira idan an samu kudade, to ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an aiwatar da shi a jihar,” inji shi.
Ya bayyana cewa sun biya ma’aikatan lafiya na jihar kason albashinsu da aka dan samu tasgaro kuma gwamnatin ta ci gaba da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya 100 don samar da ingantaccen yanayin aiki.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da ma’aikatar kula da kiwon lafiya matakin farko domin kula da jin dadin ma’aikatan lafiya.