A ranar Talata 1 ga watan Maris ne Majalisar Dattawa za ta kada kuri’a kan rahoton kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
Shugaban kwamitin, Sen.Ovie Omo-Agege, (APC-Delta) ne ya bayyana hakan a zaman majalisar nay au , bayan da aka gayyataci mambobin kwamitin zuwa taron da aka shirya gudanarwa da misalin karfe 2 na rana bayan kamala zaman majalisar.
Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya bayyana cewa za a gabatar da rahoton kwamitin duba kundin tsarin mulkin ne a zauren majalisar a ranar Laraba 23 ga watan Fabrairu, kuma za a raba kwafin ga ‘yan majalisar.
Don haka, ya yi kira ga Sanatoci da su yi nazarin rahoton kafin a duba shi, su kuma tabbatar da sun hallara a zauren majalisar a ranar 1 ga Maris don ba wa kansu damar kada kuri’a a kai.












































