Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta yi wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa Sarah Ochekpe da Raymond Dabo da Evangelist Leo Sunday Jitung daurin watanni uku a gidan gyaran hali.
Mutanen uku da aka yankewa hukuncin dai sun shafe shekaru hudu ana shari’a bisa tuhumar da ake musu na hada baki da kuma karkatar da kudade.
Sai dai hukuncin yana da zabin tarar N1,000,000.













































