Sai bayan mun gana da Buhari za mu yi magana taron APC na kasa -Gwamnonin APC

APC Governors 1
APC Governors 1

Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC ta ce ba za ta yi tsokaci kan dage babban taron jam’iyyar APC na kasa ba sai  bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata.

Kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa ya dage babban taron jam’iyyar na kasa daga ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga Maris, tare da fitar da sabon jadawalin yadda Babban taron kasa da na shiyya-shiyya zai kasance.

Bisa sabon jadawalin, za a fara gudanar da ayyukan babban taron kasa ne a ranar 24 ga watan Fabrairu tare da fitar da kwamitocin shiyyoyin.

Za a fara sayar da fom ga masu neman mukamai a ranar Laraba, 9 ga Maris, kuma za’arufe siyarwa a ranar Juma’a 11 ga Maris.

“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, mun gana a ranar Litinin kuma mun amince mu gana da Shugaba Buhari a ranar Talata don ci gaba da tattaunawa kan babban taron kasa da sauran batutuwa,” in ji Shugaban PGF, Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Bagudu.

Ya kara da cewa “Ba za mu ce komai ba kan wani jadawalin lokaci ba har sai mun ji ta bakin shugaban kasa.”

Bagudu ya ce taron na ranar Litinin ya tattauna kan abubuwan da ke faruwa a jihohi tare da duba zabukan kansiloli da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja da kuma zaben fidda gwani na gwamnan jihar Osun na ranar Asabar.

Ya kuma kara da cewa taron ya kuma tattauna hukuncin kotu da ya warware batun zaben jihar Kano na 2021 da kuma shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na kasa.

“Mun samu bayanai daga shugaban shugaban riko na jam’iyyar, Gwamna Mai-Mala Buni na Yobe,” inji shi.

Bagudu ya ba da tabbacin cewa gwamnonin APC za su ci gaba da samun amincewar ‘yan Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukansu na zabe a fili.

Ya kuma yabawa ‘yan Najeriya kan yadda suke nuna sha’awar abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar, inda ya kara da cewa taron zai ci gaba da hada kai da sauran masu ruwa da tsaki don dora shugabanci nagari.

Ya ce suna sane da yadda ‘yan Najeriya ke mutunta jam’iyyar APC, kuma ba za ta bata musu rai ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here