’Yan sanda sun cafke wasu rikakkun ’yan bindiga guda 7 ciki harda mata 2 tare da kwato kudin fansa a hannunsu a babban birnin tarayyar Abuja.
Rundunar ’yan sanda ta kama su ne da kudin fansa kimanin Naira Miliyan 9 a hannunsu da kuma makamai da rigar sulke da guraye da layoyi da kuma miyagun kwayoyi.
Kakakin rundunar CP Benneth Igweh, ya ce kudin da aka kama na fansa ne da dangin wani da suka sace suka biya.
Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya na kira da Interpol ta binciki mutane 3 kan zargin Dala Miliyan 6.2
Da yake gabatar da su a safiyar Laraba, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun fito ne daga jihohin Neja da Filato da Katsina da Kaduna da Borno da kuma Abuja.
A cewarsa, sun amsa zargin da ake musu kuma suna da hannu a garkuwa da mutane da aka yi a Abuja.
“Ana ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a kotu,” in ji shi.













































