
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol, da ta sanya mutane 3 da ake tuhuma a cikin jerin sunayen wadanda ake tuhuma da laifin zamba na Dala Miliyan 6230.
Mai bincike na musamman da shugaba Bola Tinubu ya nada domin duba lamarin ya ce wadanda ake zargin su ne Adamu Abubakar da Imam Abubakar da kuma Odoh Eric Ocheme.
Karanta wannan: Matan gwamnonin Najeriya sun bukaci kafa dokar shan miyagun kwayoyi
Mutanen 3 dai sun yi zargin karya sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu takardu da ake zargin Boss Mustapha tsohon sakataren gwamnatin tarayya SGF ne ya rubuta domin su biya Dala Miliyan 6,230,000 da ake zargin an tanadar wa masu sa ido kan zaben kasar waje daga babban bankin kasa na CBN.
Tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele da aka dakatar shi ma ana tuhumarsa da laifin zamba, kamar yadda Mustapha ya yi ikirarin a ranar Talata cewa shi ko tsohon shugaban kasa Buhari ba su amince da fitar da kudaden ga masu sa ido kan zabe na kasa da kasa ba.












































