Gwamnatin Kenya ta ce ba za ta rufe Facebook ba gabanin zabe

download
download

Gwamnatin Kenya ta ce ba za ta rufe shafin sada zumunta na Facebook ba, duk da barazanar da hukumar haɗin kan ƙasa ta yi na dakatar da shi.

A makon jiya hukumar haɗin kai ta ƙasa (NCIC) ta ce ta aika wa Meta, kamfanin da ke da Facebook, sako cewa suna neman a mayar da martani game da zarge-zargen kalaman tunzura jama’a a shafin gabanin zaben da za a yi.

NCIC ta yi barazanar dakatar da ayyukan kamfanin idan har a cikin kwana bakwai bai bi dokar da aka sa masa ta toshe kalaman kiyayyar da ke yaɗuwa a kasar ba.

Amma Ministan Fasaha ya nemi karin bayani game da tsarin dokar da NCIC ke amfani da ita domin dakatar da Facebook.

Shi ma Ministan Harkokin Cikin Gida Fred Matiang’i a wata sanarwa ta daban, ya ce gwamnati ba ta da niyyar rufe kafofin sada zumunta kuma ta nisanta kanta da sanarwar NCIC.

Sai dai a martanin da Facebook ya mayar, ya ce ya ƙara inganta hanyoyin toshe kalaman kiyayya ko kuma tunzura jama’a musamman lokacin zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here