Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Alhamis ya ziyarci garin Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’ummar yankin da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren masu garkuwa da mutane da aka kai kwanan nan.
Gwamnan ya yi addu’a ga wadanda suka rasu, tare da yabawa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tukuru wajen dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.
Haka kuma, AbdulRazaq ya aike da sakon ta’aziyya da nuna goyon baya ga sauran al’ummomin da suka fuskanci irin wannan barazana, ciki har da Ifelodun, Irepodun, Isin, Ekiti, Edu da Pategi.
Gwamnan ya bayyana cewa lamarin ya kasance mai matukar kalubale, sai dai gwamnati ta na daukar matakan da suka dace don rage illolinsa tare da tabbatar da cewa irin wannan al’amari bai sake faruwa ba a nan gaba.
A yayin ziyarar, gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, Daraktan DSS na jihar, Kwamandan NSCDC na jihar, Dr Umar Mohammed, mai taimaka masa kan harkokin tsaro, Muyideen Aliyu, da kuma shugaban karamar hukumar Ifelodun, Hon. Femi Yusuf.
Haka kuma, gwamnan ya karbi rahotanni daga jami’an tsaro da shugabannin al’umma na Oke-Ode da makwabciyar Igbaja, ciki har da shugaban kungiyar cigaban Oke-Ode, Alhaji Abdulganiyu Ajala, Elder Oyin Zubair, da kuma jagoran matasa na yankin.
Tun da fari, AbdulRazaq ya fitar da sanarwa inda ya jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa, yana mai jaddada cewa akwai bukatar daukar karin matakai don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
NAN













































