Wasu al’ummar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin nuna goyon bayansu ga kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Bakori, duk da karuwar kiran da ake yi na a sauke shi daga mukaminsa.
Rahoton Solacebase ya ce zanga-zangar ta biyo bayan kiran da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya yi na a sauke kwamishinan, sakamakon janyewar ‘yan sanda daga taron bikin ranar ‘yancin kai, wanda gwamnan ya bayyana a matsayin abin raini da tsoma bakin siyasa.
Masu zanga-zangar, karkashin jagorancin kungiyoyin da kai, sun yabawa kwamishinan bisa jajircewarsa wajen yaki da rashin tsaro, musamman matsalar satar waya da ta’addancin tituna da suka zama barazana ga al’umma a Kano.
Sun rike takardu dauke da rubuce rubuce don nuna adawa da kiran da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na a cire kwamishinan daga mukaminsa.
Shugabar kungiyar mata lauyoyi, Barista Khadija Abba Isma’il, ta ce Bakori ya fi cancantar samun karfafa guiwa fiye da a kore shi a wannan lokaci mai cike da kalubale.
Labari mai alaƙa: Najeriya@65: Gwamna Yusuf ya bukaci shugaba Tinubu ya cire kwamishinan ƴan sandan Kano
A gefe guda kuma, wata kungiyar siyasa mai suna One Kano Agenda ta zargi gwamnatin tarayya da lalata bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a Kano, ta hanyar abin da ta kira tsoma bakin siyasa daga bangaren ‘yan sanda.
A taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar kungiyar NUJ Kano, Darakta Janar na kungiyar, Abass Abdullahi Yakasai, ya ce janyewar rundunar ‘yan sanda daga filin taron biki kafin fara shagulgulan, ba kuskuren gudanarwa ba ne, illa umarnin daga Abuja don kunyata Gwamna Abba Kabir Yusuf da rage wa jama’a kwarin gwiwa.
Wannan lamari ya kara rarraba siyasar Kano, inda wasu ke mara baya ga bukatar gwamnan na a cire kwamishinan, yayin da wasu ke kare irin kokarin da ya yi wajen yaki da rashin tsaro a jihar.
NAN













































