Lauyoyin Dake Kare Abduljabbar Sun Janye Daga Shari’arsa

120582890 bbcabduljabbar
120582890 bbcabduljabbar

Tawagar Lauyoyin dake Kare malamin addinin Islama a Jihar Kano, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, wato WAK sun bayyana janyewarsu daga sharia’ar da ake yi tsakaninsa da gwamnatin jihar.

A cikin wata wasika da suka aikewa alkalin babbar kotun shari’a ta jihar Kano dake Kofar Kudu, lauyoyin sun ce janyewar ta biyo bayan tattaunawa ta musamman da suka yi a tsakaninsu ranar 14 ga watan Satumban 2021, a muhallin Gidan Gyaran Hali dake Kurmawa a Kano.

Wasikar ta ce “Bisa dalilan da suka wanzu tsakanin WAK da wannan tawaga ta Lauyoyinsa, da kuma tattaunawa ta musamman da suka yi tsakaninsu ranar 14 ga watan Satumban 2021 a muhallin Gidan Gyaran Hali dake Kurmawa Kano, gami da matsayar WAK akan wannan tawaga ta Lauyoyi, muna sanar da Kotu janyewarmu daga wannan shari’a a matsayin Lauyoyin Kariya.

Saidai sanarwar janyewa daga shari’ar da ake yi wa Abduljabbar mai lamba CR/1/2021 Da Lambar Tuhuma CR/631/2021 gwamnatin Jihar Kano Da Abduljabbar Shekh Nasir Kabara ba ta bayyana abinda suka tattauna a a ganawar da suka yi ba.

“Muna fatan Kotu zata karbi wannan janyewa tamu. Allah Ya ba Mallam ikon yin adalci”.

Sanarwar Lauyoyin

Karanta Wannan: An Kama Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Kisan Ɗan Sanata Ibn Na’allah

Lauyoyin dake kare Abduljabbar din su ne; Sale Mohammed Bakaro Esq da H.GMagashi Esq da Bashir Sabiu Esq da R. S. Abdullahi Esq da kuma Y. A. Umar Esq.

A Ranar Juma’a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here