Gwamnatin Oyo ta sanya dokar hana fita a Kananan Hukumomi 10

Oyo State Governor Seyi Makinde (1)

Gwamnatin Jihar Oyo ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10 da ke iyaka da Tsohon Dajin Oyo National Park, yayin da Gwamna Seyi Makinde ya amince da matakin a matsayin wani bangare na kokarin tabbatar da tsaro a yankunan da abin ya shafa.

A cewar wata wasika da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde ya fitar, kuma mai ba Gwamna shawara na musamman kan kafafen watsa labarai, Dr. Sulaimon Olanrewaju ya raba wa ‘yan jarida a ranar Talata, dokar hana fitan za ta fara aiki daga Laraba, 24 ga Yuni 2026.

“Dokar hana fita za ta fara aiki daga Laraba, 24 ga Yuni 2026,” in ji wasikar.

Wasikar ta kara da cewa takunkumin, wanda zai kasance daga karfe 4:00 na yamma zuwa karfe 8:00 na safe a kowace rana, “zai dauki awa 48 a mataki na farko” kuma ya shafi kananan hukumomin da ke iyaka da Tsohon Dajin Oyo National Park.

Kanana hukumomin da abin ya shafa su ne Oriire, Orelope, Irepo, Saki West, Saki East, Atisbo, Itesiwaju, Iseyin, Olorunsogo da Atiba.

Gwamnati ta roki mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi umarnin tare da ba da hadin kai ga hukumomin tsaro a lokacin takunkumin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here