‘Safarar Miyagun Kwayoyi’: Kotu ta dage shari’ar da matar da aka tsare bisa kuskure a Saudiyya ta shigar da Ethiopian Airlines da SAHCO

imgonline com ua twotoone p9DQ1HdcWtdv 750x430

‘Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ci gaba da shari’ar da wata mata ‘yar asalin Jihar Kano da aka zarge ta bisa kuskure da safar miyagun kwayoyi a Saudiyya, Bahijja Aminu Abdullahi, ta shigar da a kan Ethiopian Airlines, Skyway Aviation Handling Company Plc (SAHCO) da Ali Abubakar Muhammad zuwa 8 ga Oktoba, 2026, domin baiwa bangarorin damar tattaunawar sulhu a wajen kotu.

Shari’ar da ke gaban Mai Shari’a S.M. Shuaib na Kotu ta 1, ta samo asali ne daga lamarin da ya haddasa kama Bahijja a Saudiyya a lokacin da ta je aikin Umrah, bayan da aka danganta jaka mai dauke da miyagun kwayoyi da takardun tafiyarta.

Lauyan mai shigar da kara, Barrista Ibrahim Muhammad, ya bayyana wa SolaceBase cewa an shigar da karar ne a watan Janairu 2026, inda aka sanya Ethiopian Airlines a matsayin wanda ake kara na farko, SAHCO na biyu da Ali Abubakar Muhammad na uku.

A cewarsa, an yi nasarar mika takardun kotu ga Ethiopian Airlines da SAHCO kafin zaman kotun na farko a shari’ar, yayin da aka ci gaba da kokarin mika wa wanda ake kara na uku a lokacin.

Ya bayyana cewa a zaman sauraron karar na farko a ranar 2 ga Maris 2026, kotu ta tabbatar da cewa an mika takardun kuma ta lura cewa wadanda ake kara ba su bayyana ba ta hanyar lauyoyinsu.

Daga baya SAHCO ta shigar da ‘preliminary objection’ tana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

“Lauyan wanda ake kara na biyu ya shigar da ‘preliminary objection’, yana cewa kotun ba ta da ikon sauraron shari’ar. Mun amsa ta hanyar shigar da takardunmu, inda muka dage cewa kotun tana da cikakken iko,” in ji Barrista Muhammad.

Ya kara da cewa a zaman da aka yi ranar 7 ga Mayu, lauyan wanda ake kara na uku, Ali Abubakar Muhammad, ya bayyana a gaban kotu aka ba shi lokacin domin gabatar da amsarsa.

Bayan haka aka dage shari’ar zuwa watan Yuni domin dukkan wadanda ake kara su gabatar da amsoshinsu kuma kotu ta saurari kan ikon kotun.

Sai dai a zaman na baya-bayan nan, lauyan SAHCO ya sanar da kotu cewa kamfanin na da niyyar bin hanyar sulhu a wajen kotu.

“Lauyan wanda ake kara na 2 ya gabatar da bukata yana mai cewa sun shirya sasanta lamarin cikin lumana. Dangane da wannan bukata, kotu ta ba bangarorin lokaci don yin Nazari kan zabin sulhu,” in ji lauyan.

Mai Shari’a Shuaib ya dage shari’ar zuwa 8 ga Oktoba, 2026.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here