Taron shekara-shekara: Pantami da Bala Lau za su gabatar da jawabi a taron Ƙungiyar Musulman Najeriya ta Burtaniya

WhatsApp Image 2025 10 25 at 18.46.23 750x430

Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, zai gabatar da muhimmin jawabi a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Musulman Najeriya ta Burtaniya (NMFUK), wanda za a gudanar a birnin Manchester ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, 2025.

Jaridar olacebase ta ruwaito cewa, taken taron shi ne “Tattalin Arzikin Zamani Mai Tsarin Gaskiya: Makomar Bankin Musulunci na Zamani”, inda masana, ‘yan kasuwa da shugabanni za su tattauna kan alaƙar da ke tsakanin fasahar zamani, ɗabi’a da tsarin kuɗin Musulunci.

Daga cikin fitattun masu gabatar da jawabi akwai Dakta Abdullahi Bala Lau, shugaban ƙasa na Ƙungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), da kuma Raza Ullah, wanda shi ne shugaban kamfanin kuɗi mai tsarin gaskiya, Pfida.

Shugaban ƙasa na Ƙungiyar Musulman Najeriya ta Burtaniya, Dakta Bilyaminu Romo, ya bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne na babban taron shekara-shekara na ƙungiyar, wanda ke zama dandamali na musayar ilimi, da karfafa haɗin kai da kuma nuna darajar al’adun Musulunci.

Dakta Romo ya ƙara da cewa, za a tattauna hanyoyin da ka’idojin Musulunci za su iya jagorantar kirkire-kirkire a fannin kuɗi na zamani, ta yadda za a tabbatar da gaskiya, haɗin kai da kuma walwalar jama’a.

Haka kuma, jawabin Farfesa Pantami zai mayar da hankali ne kan yadda sabbin fasahohin zamani ke taimakawa wajen faɗaɗa damar samun kuɗaɗen Musulunci a Najeriya, wacce ke ƙara samun ci gaba a fannin tattalin arzikin gaskiya.

Ƙungiyar Musulman Najeriya ta Burtaniya (NMFUK) ƙungiya ce da ke haɗa Musulman Najeriya mazauna ƙasar Burtaniya, kuma tana gudanar da ayyukan taimako, ilimi, kiwon lafiya da tallafin marayu a Najeriya da ƙasashen waje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here