Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa rushe kwamitocin zartarwarta a Jihar Kano a dukkan matakai ya nan daram kuma ba za a iya sauya wannan mataki ta hanyar umarnin kotu ba.
Wannan na cikin wata sanarwar da Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya fitar a Abuja.
Jam’iyyar ta yi wannan bayani ne bayan jaridar Solacebase ta rawaito cewa Kotun Ƙoli ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Nasiru Saminu ta soke rushe kwamitocin zartarwa na jiha, ƙananan hukumomi da unguwanni na jam’iyyar a Kano.
Kwamitin zartarwa na ƙasa na NNPP ya sanar da rushe dukkanin tsarin jam’iyyar a Kano makon da ya gabata bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Hashim Dungurawa, tare da naɗa Abdullahi Abiya a matsayin mukaddashin shugaba.
Karanta: Kotu ta tabbatar da dakatar da Hashimu Dungurawa a matsayin shugaban NNPP na Kano
A wani umarni na wucin gadi da kotu ta bayar, an hana kwamitin zartarwa na ƙasa na NNPP ɗaukar duk wani mataki dangane da tsarin shugabancin jam’iyyar a Kano har sai an saurari ƙarar da aka shigar, tare da umarnin a ci gaba da bin matsayin da ake ciki kafin ranar da aka fitar da umarnin rushewar.
Ƙarar mai lamba K/06/2026 ta fito ne daga Abdullahi Zubairu Imam da wasu biyar a madadin kwamitocin zartarwa na NNPP a ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda suka ƙalubalanci matakin rushewar da jam’iyyar ta ɗauka.
Sai dai Ladipo Johnson ya ce rahotannin da ke cewa kotu ta soke matakin jam’iyyar jita-jita ne kawai, kasancewar jam’iyyar ba a miƙa mata kowace takardar kotu ba, don haka rushe kwamitocin zartarwa na Kano a dukkan matakai ya nan daram.
Johnson ya ƙara da cewa, a cewar hukuncin Kotun Ƙoli a shari’o’i da dama, harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa ba sa ƙarƙashin ikon kotu, don haka duk wani yunƙuri na soke matakin NNPP daga kotu ba zai yi tasiri ba.
Ya kuma kara da mai cewa idan har aka tabbatar da irin wannan umarni, jam’iyyar za ta ɗauki dukkan matakan doka da suka dace, har da kai ƙara ga Hukumar Kula da Alƙalai ta Ƙasa.
NAN













































