Gwamnan Kano zai mallaki APC a jiha idan Kwankwaso ya sauya sheƙa tare da shi – masani a siyasa

Kwankwaso and Abba 720x430 (1)

Wani fitaccen masani a fannin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayyana cewa kundin tsarin APC ya tanadi cewa gwamna mai ci shi ne jagoran jam’iyyar a kowace jiha, lamarin da zai sanya Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance a gaba da Rabiu Musa Kwankwaso a tsarin siyasar Kano idan aka samu sauya sheƙa.

Masanin ya yi nuni da cewa irin wannan tsari na shugabanci na iya zama abin da Kwankwaso ba zai amince da shi ba, duba da yadda ya dade yana da karfin tasiri a siyasar jihar tsawon shekaru da dama.

Farfesa Fagge ya bayyana cewa rikicin da ke gudana tsakanin shugabannin biyu ya dace da abin da aka saba gani a siyasar Najeriya, inda dangantaka tsakanin gwamnonin da ke kan mulki da ubangidansu na siyasa kan lalace bayan mika mulki.

Ya ce irin wadannan sabani galibi na samo asali ne daga rikice-rikice kan mallakar tsarin jam’iyya, nade-naden mukamai da kuma alkiblar manufofi, yana mai cewa abin da ke faruwa a Kano ba abu ne na daban ba, illa wani bangare ne na yanayin da ya yadu a fadin kasar.

Karanta: Tsohon shugaban APC na ƙasa Adamu har yanzu ɗan jam’iyya ne – jami’i

Masanin ya kara da cewa alamomin da ke bayyana a halin yanzu na nuna akwai babbar matsala a cikin gida tsakanin Sanata Kwankwaso da abokin siyasar da ya raina, Gwamna Yusuf, wadda ke kara dagula al’amuran jam’iyyar NNPP.

Ya kuma bayyana cewa wannan yanayi, tare da sabanin cikin gida a NNPP a matakin jiha da kasa, na iya tilasta wa gwamnan yin tunanin ficewa daga jam’iyyar domin neman wata hanya ta siyasa daban.

Game da kiran da Kwankwaso ya yi na cewa Gwamna Yusuf ya ajiye mukaminsa idan ya shiga APC, Farfesa Fagge ya ce a bisa ka’ida ta dimokuradiyya hakan ya dace, domin jama’a kan kada kuri’a ne bisa jam’iyya ba wai mutum kai tsaye ba.

Ko da yake a aikace siyasar Najeriya ta saba da wannan ka’ida, inda gwamnonin da suka sauya sheƙa ke ci gaba da rike mukamansu, abin da ke nuna raunin akidar jam’iyya da aiwatar da dimokuradiyya a cikin jam’iyyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here