NAPTIP ta tseratar da wasu mata 13 da za ayi safarar su zuwa Iraqi

NAPTIP NEW 638x430

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta samu nasarar tseratar da wasu mata 13 da ake zargin an yi safararsu, a kan hanyarsu ta zuwa Bagadaza na kasar Iraki domin yin lalata da su.

Hukumar ta NAPTIP ta ce wadanda aka kama suna tsakanin shekaru 19 zuwa 39 ne kuma an yaudare su ta hanyar cewa an dauke su a matsayin ma’aikata.

Wasu mutane ne da ake zarginsu da zama jami’an wata babbar kungiyar masu safarar mutanw da ke daukar mutane aiki a tsakanin Najeriya da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya.

Mai magana da yawun hukumar ta NAPTIP, Vincent Adekoye, ya ce an kama mutanen ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, jim kadan kafin su tashi zuwa kasar Iraqi.

Labari mai alaƙa: Wanda ake zargi da safarar mutane ya kashe kansa, yayin da NAPTIP ke tsare dashi

A halin da ake ciki, jami’an hukumar sun rufe wani shahararren otal mai suna Three Stars da ke unguwar Kwali a karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja inda aka ceto ‘yan mata 11 da ake zargi da yin lalata da su, tare da kama mai otal din yayin da sauran ma’aikatan da ke ciki suka tsere.

Wannan ci gaban dai ya zo ne bayan wata daya da hukumar NAPTIP ta kutsa kai cikin wani gida mai zaman kansa dake cikin daya daga cikin manyan gine-ginen da ke tsakiyar birnin tarayya Abuja tare da kubutar da wasu ‘yan mata masu juna biyu da ake zargi da safararsu.

Adekoye ya ce kamen da aka yi wa ‘yan matan da ake yunkurin kai su Iraqi ya biyo bayan bayanan da wasu abokan huldar da abin ya shafa suka yi, inda suka lura da yadda wasu fuskokin da ba a san ko su wanene ba suka yi dafifi a filin tashi da saukar jiragen sama tare da wasu ‘yan mata.

Da take tofa albarkacin bakinta akan lamarin, Darakta-Janar ta hukumar NAPTIP, Binta Bello ta nuna rashin jin dadinta kan yadda barayin ke damfarar jama’a, ta kuma yi kira ga iyaye da masu kula da su da su rika kula da ‘ya’yansu a unguwanni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here