Majalisar Malamai ta yi watsi da zargin da ake yiwa wasu matasa 2 a Filato na zama yan kungiyar ISWAP

Plateau map (1)

Majalisar Malamai a garin Yelwa da ke karamar hukumar Shendam a jihar Filato, ta yi kakkausar suka ga ikirarin cewa wasu matasa teloli biyu daga garin ‘yan kungiyar IS ne a lardin yammacin Afirka, inda ta bayyana zargin a matsayin rashin adalci.

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban majalisar Imam Abdulkarim Salihu ya sanya wa hannu da sakatarenta Imam Abubakar Nuhu Gambo da kuma ma’ajinta Imam Armaya’u Abdulkadir Ismail a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, an bayyana sunayen telolin guda biyu Abdulkadir Dalhatu mai shekaru 25 da Ubaidu Hassan mai shekaru 25 a cikin wata sanarwa da rundunar ‘Operation Safe Haven’ ta fitar a ranar Asabar, 12 ga watan Afrilu, inda ta ce dakarunta sun kama wadanda ake zargin ‘yan kungiyar ISWAP ne, tare da kashe wani dan bindiga da kwato makamai a wani samame da suka kai a Yelwa.

Karanta: Ku dawowa da Jihar Rivers Naira miliyan 300 na karbar bakuncin babban taron shekara -Ibas ya fadawa NBA

Sanarwar wadda Manjo Samson Nantip Zahkom, jami’in yada labarai na rundunar ya sanyawa hannu, ya yi zargin cewa an kama matasan ne a lokacin da suke ikirarin su teloli ne a wani samame da aka yi a ranar 11 ga Afrilu.

Sai dai majalisar ta yi watsi da wannan ikirari, inda ta dage cewa ba a gudanar da irin wannan aiki a Yelwa ba a ranar da aka bayyana.

Maimakon haka, sun ba da labarin wani abin da ya faru a ranar 10 ga Afrilu, lokacin da wani mutum da ba a san ko wanene ba ya shigo unguwar, ya fara daukar hotuna a gaban shagon telolin da ke gidan Abdullahi Baraya a kan titin Ibbi.

Bayan da mutanen yankin suka yi masa tambayoyi kan zarginsa da kuma kin bayyana kansa da kyau, mutumin ya kira jami’an tsaro.

Karin karatu: Kotu ta dage sauraron karar neman a dakatar da rabon ƙananan hukumomin Kano

Daga bisani ‘yan sanda sun kama teloli biyun da wani dattijo mai suna Suleiman Abdullahi Baraya, inda daga bisani aka mika su zuwa barikin Sojoji na 332 na Artillery Regiment da ke Shendam domin amsa tambayoyi.

SolaceBase ta ruwaito cewa majalisar ta ce Baraya, wanda aka sake shi, an sanar da shi cewa mutumin da ba a san ko wanene ba, wani jami’in leken asiri ne da ake zargi da bin diddigin wani da ake zargin dan ta’adda ne da aka ce ya ziyarci shagon dinkin wani lokaci da ya wuce.

Sanarwar ta kara da cewa, “Mun yi matukar kaduwa da ganin hotunan wadannan samari biyu, wadanda aka san su a daukacin al’ummar Yelwa da kyawawan halaye da kuma gaskiya, ana yada su a kafafen yada labarai a matsayin ‘yan kungiyar ta’addanci.”

Majalisar Malamai ta jaddada cewa, Abdulkadir da Ubaidu dukkansu mutane ne masu bin doka da oda, don haka ta bukaci hukumomin soja da su gudanar da lamarin cikin kwarewa da gaskiya.

Sun kuma yi kira da a gaggauta sakin matasan da ake tsare da su, tare da lura da cewa ci gaba da tsare su yana kawo cikas ga rayuwarsu da rashin adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here