Wani babban alkalin kotun Majistire a jihar Rivers, Ejike King George, ya yi murabus bisa radin kansa, saboda rashin jin dadi da nadin da ya bayyana shi a matsayin “gwamnatin soji” da ta sa ido kan al’amuran jihar.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 11 ga Afrilu, 2025, kuma aka aika wa mai girma Alkalin Alkalan Jihar Rivers ta hannun Sakataren hukumar kula da Shari’a ta jihar Rivers, Majistare George ya nuna rashin jin dadinsa game da alkiblar tafiyar da mulkin Jihar, inda ya bayyana cewa hakan cin fuska ne ga kimar aikin Shari’a.
Da yake karin haske kan shekarun da ya yi na aikin Shari’a, George ya lura cewa ya sadaukar da shekaru 16 a cikin shekaru 22 da ya yi yana aikin shari’a ga bangaren shari’a na Jihar Rivers a matsayin Alkali a karkashin gwamnatocin dimokuradiyya daban-daban.
Ya bayyana damuwarsa cewa, ci gaba da zama a karkashin tsarin yanzu zai kai ga rashin yarda.
George ya ƙare wasiƙarsa da godiya.