Hukumar Kwastam ta yi gwanjon motoci da ta kama a Katsina

NCS auctions seized vehicles in Katsina 768x508 1
NCS auctions seized vehicles in Katsina 768x508 1

A Juma’ar nan ne hukumar yaƙi da fasa kwari ta Najeriya Kwastam shiyyar jihar Katsina, ta yi gwanjon ɗaruruwan motocin da ta kama waɗanda ake amfani da su wajen yin fasa kwaurin kayayyaki a jihar.

Muƙaddashin shugaban hukumar na Katsina, Alhaji Dalha Wada-Chedi, a lokacin da yake zantawa da manema labarai ya ce, matakin ya yi dai-dai da umarnin shugaban hukumar na ƙasa Kanal Hamid Ali mai ritaya.

Haka kuma, Ya bayyana cewa hukumar ta bayar da umarnin yin gwanjon motocin waɗanda aka yi watsi da su a matsayin tarkace don haka masu sha’awar yin amfani da su sai su saya.

Wada Chedi ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da hukumar ta yi gwanjon irin waɗannan motoci ba.
“An yi atisayen gwanjon ne ta hanyar yin amfani da ka’idojinmu waɗanda za su ci moriyar za su ragargaza motoci ne.

“Manufar yin haka ita ce samar wa kamfanonin karafa da albarkatun ƙasa, rage fasa-kwauri, da rage cunkoso a wurarensu da samar da ayyukan yi,” inji shi.

Mista Chukwube Ofoma, wanda ya sayi wasu motocin, ya bayyana cewa ya biya kuɗi ne asusun gwamnatin tarayya na motocin, yana mai cewa hakan wani ci gaba ne mai kyau.

Alhaji Garba Sheka, da ya saya, ya yaba wa gwamnatin tarayya da ta ba su damar siyan tarkace motocin inda ya yi nuni da cewa hakan zai bunƙasa sana’ar mu da kuma taimakawa wajen samar da ayyukan yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here