Yan bindiga sun hallaka Jami’ai 3 a wani hari da suka kai Ofishin ‘Yan sanda, a Kogi

Gunmen
Gunmen

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe Jami’an tsaro 3 a wani hari da suka kai hedikwatar ‘yan sanda dake Adavi a jihar Kogi.

Jaridar Solacebase  ta rawaito cewa, shugaban karamar hukumar Adavi, Joseph Omuya Salami, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban karamar Hukumar kan harkokin yada labarai Injiniya M. Jamiu Habeeb ya fitar a ranar Asabar ya ce,’’ shugaban karamar hukumar Adavi, Honorable Joseph Omuya Salami ya tabbatar da cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun farmaki dakarun sashen kai daukin gaggawa da aka tura zuwa Kogi ta tsakiya a hedikwatar ‘yan sanda ta Adavi inda suka kashe jami’ai uku a yayin musayar wuta.

Ya ce shugaban karamar hukumar ya garzaya ofishin ‘yan sandan da misalin karfe 12:45 na daren ranar Juma’a lokacin da ya samu rahoton aukuwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here