Jami’ar Bayero ta kori dalibai 62, ta hukunta wasu 17

BUK 1 3

Jami’ar Bayero ta Kano ta kori dalibai 62 tare da ɗaukan matakin hukunta wasu 17 bisa zarginsu da satar jarrabawa.

SolaceBase ta ruwaito cewa majalisar zartarwar jami’ar ta amince da hukuncin ladabtarwa a taronta na 421 da ta gudanar a ranar Laraba, 26 ga Fabrairun 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da jami’ar ta fitar na mako-mako a ranar Juma’a.

Karanta: Jami’ar Tarayya a Dutse ta nada Abdullahi Bello a matsayin darakta mai kula da harkokin jama’a

Hukuncin ya amince a hukunta dalibai 17, tare da wanke dalibai 5 sai kuma ɗalibai 29 da aka yiwa gargadi, an kuma dage shari’ar wasu uku.

Sanarwar ta ce an yanke hukuncin ne bisa ka’idar jarrabawar kammala karatun jami’a (GEAR).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here