Jami’ar Tarayya a Dutse ta nada Abdullahi Bello a matsayin darakta mai kula da harkokin jama’a

WhatsApp Image 2025 03 07 at 13.41.36 750x430

Mataimakin shugaban Jami’ar tarayya Dutse, da ke kihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammed, ya amince da nadin Malam Abdullahi Yahaya Bello a matsayin Darakta na riko na Jami’ar daga ranar 1 ga Maris 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar jami’ar ta fitar a ranar Juma’a.

Shugaban jami’ar a cikin takardar nadin da magatakardar jami’ar, Alhaji Abubakar Mijinyawa ya sanyawa hannu, ta taya wanda aka nada, tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi nasara wajen sauke nauyin da aka dora masa.

SolaceBase ta ruwaito cewa Mal. Abdullahi ya kammala karatu a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero Kano a shekara ta 2000, kuma ya na da gogewa na shekaru 25 bayan kammala karatunsa a matsayin malami kuma dan jarida sannan jami’i mai hulda da jama’a.

Karin karatu: A taimaka a biya mana kudin makaranta kafin a sallame mu-Daliban Kano na FUD

Shi kadai ne ya kafa sashen yada labarai da hulda da jama’a na Jami’ar a shekarar 2012 a matsayin jami’in hulda da jama’a na Jami’ar na farko. Ya samu matsayi har ya zama Mataimakin Daraktan Sashen yada Labarai da Hulda da Jama’a na farko a shekarar 2023 kafin a nada shi a matsayin Daraktan hulda da jama’a na Jami’ar tarayya ta Dutse na farko.

Ya halarci shirye-shiryen horar da kafafen yada labarai da hulda da jama’a da dama, Shi mataimaki ne a Cibiyar hulda da jama’a ta kasa (NIPR), Memba a kungiyar ‘Yan jarida ta kasa (NUJ), Memba a kungiyar masu gudanar da jami’o’in Najeriya (ANUPA) kana Memba a cibiyar gudanar da mulki ta kasa (IRAMN).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here