Sojoji sun kashe jagoran Lakurawa, Maigemu a jihar Kebbi

army repels boko haram attack in borno

Tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sintiri sun yi nasarar kawsge jagoran yan ta’addar Lakurawa Maigemu a Kebbi.

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na jihar, Alhaji AbdulRahman Usman-Zagga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Birnin Kebbi.

Ya ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, wani yanki mai nisa da ke da kalubale, bayan an yi artabu da bindiga.

Ya kara da cewa “wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a karamar hukumar Arewa domin jajantawa mazauna garin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa sun yi.

Karanta: An Kashe Mazauna Wani Kauye Da Dama Yayin Wani Harin Jirgin sojojin Najeriya Da Ya Kai Kan Lakurawa A Jihar Sokoto

“A ziyarar da gwamnan ya kai, ya tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa na karfafa tsaro cikin gaggawa tare da daukar matakan da suka dace don magance ayyukan miyagun laifuka a yankin”.

“A yau, matakin da ya ɗauka ya haifar da sakamako tare da kawar da wannan jagora, kuma Gawar sa tana nan a matsayin shaida,” in ji Usman-Zagga.

Ya kuma yabawa gwamnan bisa jajircewar sa wajen samar da tsaro da kuma ci gaba da bayar da tallafin kayan aiki ga jami’an tsaro musamman masu gudanar da ayyuka na musamman.

Daraktan ya bukaci mazauna yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai ta hanyar basu bayanan sirri da kuma bayar da rahoton wasu abubuwan da ake zargi domin samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Lakurawa dai wata kungiyar ta’addanci ce da ta kutsa kai cikin jihohin Sokoto da Kebbi da suke iyaka da Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here