A safiyar Larabar ne wani jirgin yaki na sojojin saman Najeriya ya kai hari wa ‘yan ta’adda Lakurawa, a wasu kauyuka biyu masu a karamar hukumar Silame da ke jihar Sokoto a safiyar ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar yan ba ruwana da dama tare da jikkata wasu da dama.
Shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya bayyana lamarin a matsayin mai muni, inda ya ce wadanda abin ya shafa ba su da wani laifi.












































