Majalisar dattijai ta dakatar da sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Udughan na tsawon watanni shida.
Ta samu rinjayen kuri’u bisa amincewa da shawarwarin kwamitin da’a, gata da ka’idojin da’a na majalisar dattawa.
A yayin zaman majalisar, an hana Akpoti-Uduaghan damar yin magana a gaban Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattijai wanda ya nemi a kada kuri’a.
Sun kuma kada kuri’ar kada a sake duba zaben kafin wa’adin watanni shida ya cika ko kuma ta nemi gafara.
Neda Imasuen, shugaban kwamitin, ya karanta shawarwarin yayin zaman majalisar.