Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ya mika takardar shaidar sarautar ga sarki kuma sabon Alaafin na Oyo a safiyar ranar Litinin a dakin taro na Exco Chamber na ofishin gwamna dake Ibadan.
Gudanar da gagarumin taron na zuwa ne kusan shekaru uku da rasuwar tsohon Alaafin, Lamidi Adeyemi na III.
Gwamna Makinde ya gabatar da shaidar kama aikin ne a yayin da ake ta cece-kuce game da zaben sabon Alaafin da gwamnan ya bayyana a makon jiya.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Dotun Oyelade, ya ce Owoade bayan bincike da tuntuba, Oyomesi ya ba da shawara kuma gwamnan ya amince da shi.
Ya ce sanarwar ta janyo cece-kuce tun bayan rasuwar Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III a ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Kwamishinan ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Oyo da su hada kai da gwamnati wajen gudanar da wannan gagarumin biki tare da bayar da goyon bayansu ga sabon Alaafin na Oyo.