Najeriya Tayi Asarar Dukiya Ta ₦67.1bn, da rayuka 100 a gobara a 2024 – Jaji

Abdulganiyu Jaji Fire 750x430

Hukumar kashe gobara ta tarayya ta tabbatar da kiyasta cewa an tafka asarar dukiya ta Naira biliyan 67.1, kuma asarar rayuka a shekarar 2024 sakamakon barkewar gobara.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce babban kwamandan hukumar, Abdulganiyu Jaji a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar Hukumar da ke Abuja, ya kara da cewa akalla mutane 100 ne suka mutu sakamakon tashin gobara a cikin wannan lokacin.

Jaji, ya ce hukumar ta ceto kadarorin da ya kai Naira tiriliyan 1.94 a shekarar bara da ta gabata.

“A shekarar 2024, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta yi nasarar ceto kadarorin da ya kai Naira Tiriliyan 1.94 tare da yin asarar dukiyoyin da aka kiyasta ya kai Naira biliyan 67.1.

Jaji, wanda ya ce matsalar barkewar gobara na iya karuwa a lokacin sanyi da iska, lokacin da zafi ya yi rauni, ya roki dukkan masu gudanar da aikin gidajen mai, tankunan mai, tasoshin mai da iskar gas, masu amfani da iskar gas da sauran jama’a da su rinka bin ka’idoji.

“Za mu mai da hankali kan wayar da kan jama’a, da kuma inganta ayyukan mu ta hanyar amfani da fasahohin zamani” in ji shi.

A yayin da yake yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan amincewa da sayan na’urorin kashe gobara na zamani da kuma gyaran makarantar horas da kashe gobara, ya kira ‘yan Najeriya da su goyi bayan sake kafa dokar hukumar kashe gobara ta 1963, yana mai cewa: “Idan an cimma hakan, zai farfado da cigaban ayyukan hukumar cikin gaggawa .”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here